in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
G20 ta jaddada kara yin hadin gwiwar tattalin arziki da hada-hadar kudi a tsakanin kasa da kasa
2017-03-19 13:47:07 cri
A jiya 18 ga wata a birnin Baden Baden na kasar Jamus, aka kammala taron ministocin kudi da shugabannin bankunan tsakiya na kungiyar G20, inda aka jaddada cewa, ya kamata a kara yin hadin gwiwar tattalin arziki da hada-hadar kudi a tsakanin kasa da kasa, da yin amfani da manufofin kudi da hada-hadar kudi, da kuma yin kwaskwarima kan tsarin don cimma burin bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa.

Wannan ne taron ministocin kudi da shugabannin bankunan tsakiya na farko, tun bayan da kasar Jamus ta zama kasar dake jagorantar kungiyar G20 a wannan karo, inda bangarori daban daban suka tattauna batutuwan da suka shafi yanayin tattalin arzikin duniya, da kafa tsarin bunkasuwar tattalin arziki mai karfi da dorewa da adalci, da sa kaimi ga zuba jari a Afrika, da kafa tsarin hada-hadar kudi na duniya, da dai sauransu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China