wata sanarwar hadin gwiwa da shugabannin uku suka fitar, ta ce zurfafa hadin gwiwa a fannin cinikayya tare da samar da dabaru a cikin gida da za su mara masa baya, zai taimaka wajen habaka samun kudin shiga da ci gaba a duniya, tana mai cewa wannan na bukatar shugabannin duniya da za su halarci taron G20 su dauki nagartattun matakai.
Babbar daraktar IMF Christine Lagarde da shugaban Bankin Duniya Jim Yong Kim da darakta janar na WTO Roberto Azevedo, sun ce tun daga farko-farkon shekarun 2000, harkokin cinikayya suka tsaya wuri guda, saboda shingayen cinikayya da suka yi yawa da kuma sauran ka'idoji da ke taimakawa masana'antu na cikin gida kadai tare da kara kirkiro wasu sabbin shingayen. (Fa'iza Mustapha)