in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi taron ministocin kudi da gwamnonin manyan bankunan kasashen G20
2017-04-23 13:06:57 cri
An yi taron ministocin kudi gami da gwamnonin manyan bankunan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya wato G20 daga ranar 20 zuwa 21 ga wata a birnin Washington na kasar Amurka.

Taron ya mai da hankali ne kan wasu muhimman batutuwa, ciki har da yanayin tattalin arzikin duniya da tsare-tsaren hada-hadar kudi na duniya da bunkasa zuba jari a Afirka da dai sauransu.

Ministan kudin kasar Sin Xiao Jie, da gwamnan babban bankin kasar Zhou Xiaochuan sun jagoranci wata tawaga da ta halarci taron, inda Xiao Jie ya ce, tun daga farkon shekarar nan da muke ciki, tattalin arzikin kasar Sin ya ke samun tagomashi.

Ya ce daga watan Janairu zuwa Maris, tattalin arzikin kasar Sin ya karu da kashi 6.9 cikin dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara.

Mista Xiao ya kuma yaba da shawarar da taron G20 ya yanke, wanda ya nemi a kara zuba jari a kasashen Afirka, yana mai cewa, ya kamata kasashen G20 su karfafa hadin-gwiwa da kasashen Afirka, a kokarin cimma moriya tare, da bayar da gudummawa ga dauwamammen ci gaban tattalin arzikin Afirka da ma na duniya baki daya.

Minista Xiao Jie ya ce, akwai kasashen G20 da dama da ke zuba jari da hada-gwiwa da kasashen Afirka a halin yanzu, kuma a nan gaba, dole ne a karfafa irin wannan hadin-gwiwa domin kara zuba jari a Afirka.

A nasa bangaren, mataimakin gwamnan babban bankin kasar Sin Yi Gang ya ce, a yanzu, kasar Sin ta hada hannu da kasashen Afirka a fannin zuba jari, kuma bangarorin biyu na kokarin samun ci gaba tare, da mai da hankali kan kiyaye muhalli da kyautata zaman rayuwar al'umma, lamarin da ya ce ya samu nasarori da dama.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China