Tuni dai kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya shaidawa manema labarai cewa, kasar Sin na fatan wannan taro, zai mai da hankali wajen karfafa hadin-gwiwa, da tunkarar manyan kalubalen da kasashe da dama ke fuskanta, tare da kara daidaita harkokin duniya, da kuma raya tattalin arzikin duniya ta hanyar da ta dace, wadanda batutuwa ne dake da matukar muhimmanci ga kasashe daban-daban a halin yanzu.
A cikin wata sanarwar da ya fitar gabannin taron, mataimakin firaministan kasar Jamus, kana ministan harkokin wajen kasar, Mista Sigmar Gabriel ya bayyana cewa, yana fatan taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 gami da taro karo na 53 kan harkokin tsaro da za a yi nan ba da jimawa ba a birnin Munich, za su tattauna kan matakan da kasashe za su dauka na tunkarar manyan kalubale a fadin duniya.(Murtala Zhang)