Mataimakiyar firayin ministan kasar Sin Liu Yandong ta yi kira ga kasashen duniya da su kara hada kai, tare da yin musaya a bangaren dakunan ajiye kayan tarihi.
Madam Liu ta yi wannan kiran ne a jiya Alhamis lokacin da ta ke jawabi a bikin bude taron dandalin dakunan kayan tarihi na kasa da kasa da ya gudana a birnin Shenzhen dake lardin Guangdong a nan kasar Sin. Bayanai na nuna cewa, ana baje kolin muhimman kayayyakin tarihi a irin wadannan dakunan ajiye kayan tarihi har sau 20000 a ko wace shekara, inda baki daga sassan duniya daban-daban kimanin miliyan 700 suke ziyarta, baya ga muhimmayar rawar da dakunan ke takawa wajen bunkasa harkokin jin dadin jama'a da na tattalin arziki.(Ibrahim)