in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na sa himma wajen kiyaye kayayyakin al'adun gargajiya dake dab da bacewa a duniya
2016-12-04 14:14:24 cri
Wakilin gwamnatin kasar Sin, kuma shugaban hukumar kayayyakin tarihi na kasar Mista Liu Yuzhu ya bayyana cewa, kiyaye kayayyakin al'adun gargajiya dake dab da bacewa wani muhimmin aiki ne na gaggawa na kiyaye kayayyakin tarihi na dan Adam, gwamnatin kasar Sin na son sa himma wajen shiga aikin kiyaye kayayyakin al'adun gargajiya dake dab da bacewa a duniya.

Mista Liu ya bayyana haka ne a yayin taron kasa da kasa game da kiyaye kayayyakin al'adun gargajiya dake dab da bacewa da aka shirya daga ranar 2 zuwa 3 ga wata a Abu Dhabi, babban birnin kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, taron da aka shirya a karkashin shawarar kasashen Faransa da Hadaddiyar Daular Larabawa, da nufin nuna goyon baya da karfafa aikin kiyaye kayayyakin al'adun gargajiya na duniya ta hanyar kafa asusun kasa da kasa, da hada kai tsakanin kasa da kasa wajen kiyaye al'adun tarihi. Babbar daraktar kungiyar UNESCO Irina Bokova ta ba da jawabi a yayin bikin bude taron, kuma shugaban kasar Faransa François Hollande, yarima mai jiran gadon sarautar Hadaddiyar Daular Larabawa Khalid Sheikh Mohammed sun yi jawabi a yayin bikin rufe taron.

Liu ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin na mayar da hankali sosai kan wannan taro, tana kuma nuna yabo ga kokarin da UNESCO, gwamnatocin Faransa da Hadaddiyar Daular Larabawa suka yi domin wannan taro.Ya ce, gwamnatin kasar Sin za ta sauke nauyin dake kanta, za ta karbi kayayyakin al'adun gargajiya dake dab da bacewa don gudun hadarurruka, kana za ta kara wa kamfanonin kasarta da basu goyon baya don su samar da taimako ga asusun kiyaye kayayyakin al'adun gargajiya dake dab da bacewa na duniya. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China