in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Amurka a Jamus
2017-07-09 13:30:16 cri

A jiya Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump a birnin Hamburg na kasar Jamus, bayan da aka kammala taron ganawar shugabannin kungiyar G20, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan wasu batutuwan dake shafar kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

A yayin ganawar tasu, shugaba Xi ya bayyana cewa, a nan gaba, ya kamata kasar Sin da kasar Amurka su ci gaba da raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, bisa ka'idojin nuna girmamawa ga juna da kuma cimma moriyar juna. Haka zalika, ya kamata a inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, da kuma kara yin shawarwari kan manyan batutuwan dake shafar kasa da kasa da na shiyya-shiyya, ta yadda za a tabbatar da bunkasuwar dangantaka a tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata.

Za a gudanar da taron shawarwari kan tattalin arziki a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka a ranar 19 ga wata, sa'an nan, za a yi taron shawarwari kan harkokin tsaron intanet, da zamantakewar al'umma da kuma al'adu a tsakanin kasashen biyu a nan gaba.

Haka kuma, shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata kasashen biyu su nuna girmamawa ga juna, yayin warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyoyin da suka dace.

A nasa bangare kuma, Mr. Trump ya ce, a halin yanzu, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tana bunkasuwa cikin yanayi mai kyau. Kuma, kasar Amurka tana sa ran karfafa ma'amalar dake tsakaninta da kasar Sin bisa fannoni daban daban domin inganta hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu, ta yadda za a cimma moriyar juna. Haka kuma, kasar Amurka tana son kara yin shawarwari kan wasu batutuwan dake shafar kasa da kasa da kuma shiyya-shiyya.

Bugu da kari, shugabannin biyu sun yi musayar ra'ayoyi kan batun nikiliyar zirin Koriya, inda shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, sau da dama, kasar Sin ta taba nuna matsayinta kan wannan batu, watau, a lokacin da kasashen duniya ke mayar da martini kan matakan nuna adawa da kuduran MDD da kasar Koriya ta Arewa ta dauka, a sa'i daya kuma, ya kamata a dukufa wajen ciyar da shawarwari gaba kan wannan batu, domin sarrafa halin da ake ciki a yankin.

Daga bisani, shugaba Xi ya sake jaddada kin amincewar kasar Sin kan girke na'urorin THAAD a kasar Koriya ta Kudu.

Daga karshe, shugabannin biyu sun cimma ra'ayi daya kan ci gaba da shawarwari a tsakaninsu kan batun nukiliyar zirin Koriya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China