Xi Jinping wanda ya jagoranci kwarya kwaryar taron, ya kuma bayyana bukatar kara azama tsakanin kasashe mambobin kungiyar BRICS, a fannin warware dukkanin sabani da ake fuskanta tsakanin sassa daban daban na duniya cikin lumana, yana mai cewa akwai bukatar amfani da inuwar kungiyar G20, wajen karfafa hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin sassa daban daban.
A na su bangaren, shugabanni mahalarta taron sun sha alwashin hada kai da juna, wajen ganin an cimma sakamako mai inganci, a taron kungiyar ta BRICS dake tafe nan gaba cikin wannan shekara, wanda kuma aka tsara gudanarwa a birnin Xiamen dake kudu maso gabashin kasar Sin.(Saminu Alhassan)