in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Ya kamata sassan masu ruwa da tsaki a batun zikin koriya su koma teburin shawara
2017-05-02 19:27:55 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya yi kira ga sassan masu ruwa da tsaki game da batun zirin Koriya, da su sake bude kofar shawarwari, matakin da a cewar sa shi ne kadai zai share fagen raba yankin da makaman Nukiliya, ya kuma tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da luma, tare da kawar da sauran kalubale na tsaro da ake fuskanta a zirin.

A 'yan kwanakin baya bayan nan ne dai shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana yiwuwar tattaunawa tsakanin kasar sa da shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un, domin warware rashin jituwa dake tsakanin kasar sa da kasashen yamma.

Bisa hakan ne kuma Mr. Gang ya bayyana cewa, a matsayin Amurka da Koriya ta Arewa na kasashe masu ruwa da tsaki a batun Nukiliya a zirin Koriya, ya dace su gudanar da shawarwari a siyasance, su kuma yanke shawarwari ba tare da bata lokaci ba, domin kau da duk wani kalubale da ake fama da shi yanzu haka a zirin.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China