in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Koriya ta Arewa ta yi Allah wadai da sabuwar manufar Amurka ta mayar da ita saniyar ware
2017-04-25 20:51:32 cri
Rahotanni daga kamfanin dillancin labaran kasar Koriya ta Arewa na cewa, ma'aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah wadai da wasu sabbin matakan kasar Amurka, na rura wutar kyamar Koriya ta Arewa, gami da mayar da ita saniyar ware a fadin duniya. Wannan ya sa Koriya ta Arewa ta gargadi Amurka cewa, abun da ta shuka, shi za ta girba.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ya ce, a halin da ake ciki yanzu a zirin Koriya, irin wannan abun da Amurka ta yi, zai rura wutar yake-yake, abun da ke da hadari sosai. Amurka ta dade tana maida Koriya ta Arewa saniyar ware, da yi mata barazanar nukiliya, lamarin da yake sa Koriya ta Arewa ta kara kokarin raya makaman nukiliya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China