Taro kan makamashi na Nijeriya dake karatowa, zai mai da hankali ne kan kalubalen iskar gas da lantarki a kasar.
Wani babban jami'in cibiyar injiyoyin lantarki ta kasar Adekunle Makinde ya bayyanawa manema labarai a Lagos cewa, ayarin malamai da masu bincike matasa daga kasashen waje da hadin gwiwar cibiyar ne suka shirya taron.
Ya ce, taken taron wanda zai gudana daga ranar 4 zuwa 5 ga watan Yuli shi ne "makamashi mai dorewa don raya tattalin arziki".
A cewar Adekunle Makinde, taron kwararru da za a yi a wani bangare na babban taron, zai lalubo hanyoyin magance kalubalen a bangarorin iskar gas da lantarki da kasar ke fuskanta tare da sake inganta bangaren lantarki.
Jami'in ya ce, taron zai kunshi bada horo kan tsare-tsaren lantarki daga cibiyar bincike ta Manitola HVDC ta Canada da hanyoyin samar da lantarki daga hasken Rana wanda kamfanin Blue Camel Energy na Nijeriya zai yi da kuma hanyoyin raya makamashi daga cibiyar IEE Smart Village na Amurka.
Ya kara da cewa, mukaddashin shugaban kasar Yemi Osinbajo zai gabatar da mukala yayin taron. (Fa'iza Mustapha)