in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta tattara kudade don samar da makamashi ta hanyar tururi a Afirka
2017-07-03 13:19:18 cri

Kungiyar tarayyar Afirka tare da abokan huldarta sun tara tsabar kudi kimanin dala miliyan 150 domin samar da makamashi ta hanyar amfani da zafin dake karkashin kasa a wasu kasashe dake gabashin Afirka.

Babban jami'in sashen samar da makamashi da ababan more rayuwar jama'a na kungiyar AU Rashid Ali Abdallah ne ya sanar wa taron manema labarai yawan wadannan kudade, a gefen taron kolin kungiyar ta AU karo na 29 dake gudana yanzu haka a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Kasashen da ake sa ran za su fara cin gajiyar wannan shiri sun hada da Djibouti, Habasha, da Burundi, da Rwanda, da Kenya, inda bayanai ke nuna cewa, yankin gabashin na Afirka kadai yana iya samar da mega watts 20,000 na wutar lantarki daga wannan tsari, amma yanzu haka mega watts 500 ne kawai ake da shi a nahiyar, kuma galibi an karkata shi zuwa kasar Kenya.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China