Wani kwararren masanin muhalli dake aiki a shirin raya cigaba na MDD (UNDP) Biplove Chaudhary, ya shedawa wakilan kasashen dake halartar taro game da sauyin yanayi da samar da abinci da aka gudanar a Juba babban birnin kasar Sudan ta kudu, ya ce akwai bukatar gwamnatocin su rungumi harkar aikin gona na zamani da tattalin albarkatun kasa domin kaucewa matsalolin dake haddasa sauyin yanayi.
Chaudhary ya kara da cewa, rashin samun ingantattun kasuwanni sayar da kayayyakin aikin noma, da karancin zuba jari a fannin samar da kayayyakin more rayuwa suna daga cikin dalilan da suka haifar da koma baya ga sha'anin hada hadar kayan amfanin gona.
David Smith daga shirin kare muhalli na MDD (UNEP) ya bayyana cewa, zaman lafiya da kwanciyar hankali a siyasance ya dogara da yadda ake amfani da albarkatun kasa yadda ya kamata.
Smith, ya kara da cewa, giggina irin wadannan cibiyoyin zai dauki sama da shekaru 10 don haka ya bukaci gwamnatocin kasashen na Afrika, da MDD da sauran abokan hulda na kasa da kasa da su hanzarta tsara wadannan muhimman batutuwa.(Ahmad Fagam)