Mr. Liu wanda ya bayyana hakan yayin taron da kwamitin sulhu na MDD ya gudanar game da batun na cinikayyar kanana da matsakaitan makamai, ya kara da cewa a halin yanzu, yanayin tsaro na sauyawa, kana ra'ayin ta'addanci na kara yaduwa, baya ga yawaitar kungiyoyi masu aikata laifuffuka a duniya, don haka cinikin kanana da matsakaitan makamai na kara kawo illa ga halin da ake ciki.
Liu Jieyi ya kara da cewa, ya kamata kwamitin sulhun ya ci gaba da taka muhimmiyar rawa, wajen sa kaimi ga kasashen duniya, ta yadda za su iya samun nasarar yaki da cinikin kasana, da matsakaitan makamai, don magance mummunan tasirin da wannan matsala ke haddasawa a duniya.
Haka zalika Mr. Liu ya ce, kasar Sin na fatan ci gaba da kokari tare da kasashe daban daban, a fannin sa kaimi ga warware matsalar cinikin irin wadannan makamai, da magance tattara makaman, da kuma kawar da yiwuwar wuce gona da iri wajen yin amfani da su. (Zainab)