in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 5 sun rasu sakamakon harin ta'addanci a Burtaniya
2017-03-23 10:20:07 cri
Jiya Laraba da yamma, an kai harin ta'addanci a wurin dake kusa da babban ginin majalisar dokokin kasar Burtaniya dake birnin London.

Sa'an nan, a daren ranar, rundunar 'yan sandan birnin London ta sanar da cewa, harin ta'addanci ya haddasa rasuwar mutane 5, yayin da kimanin mutane 40 suka jikkata.

Firaministar kasar Theresa Mary May, ta kira taron kwamitin daidaita hadari cikin gaggawa a daren, inda suka tattauna game da yadda za a fuskanci wannan al'amari.

Bayan taron, firaministar ta fidda sanarwa cewa, an yi Allah wadai da kakkausar harshe kan harin ta'addancin da aka kaddamar, lamarin da ya kasance mugun harin da ba za a yi hakuri ko kadan ba a kai.

Bugu da kari, Ms. May ta ce, ba wanda zai iya canja tunanin al'ummomin kasar Burtaniya ta hanyar tashe-tashen hankula a kasar.

Bayan aukuwar harin, an rufe ginin majalisar dokokin kasar, sa'an nan, 'yan sanda sun kulle wuraren dake kusa da wurin da kuma tashar jirgin kasa dake karkashin kasa ta Westminster dake kusa da ginin majalisar dokoki.

Bugu da kari, rundunar 'yan sanda ta sanar da gargadi cewa, kada a je wuraren dake kusa da cibiyar birnin na London. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China