in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba a samu ci gaba ba wajen shawarwarin zaman lafiya kan batun Syria zagaye na 6
2017-05-20 13:46:00 cri
Ba tare da cimma wata kwakwarar matsaya ba, an kawo karshen tattaunawar zaman lafiya kan rikicin Syria zagaye na 6 dake karkashin jagorancin MDD jiya Jumma'a a birnin Geneva.

Yayin taron manema labaru da aka shirya bayan tattaunawar, manzon musamman na babban sakataren MDD dake kula da batun Syria Staffan de Mistura ya ce, bangarori daban-daban mahalarta taron sun tattauna kan wasu batutuwa na musammam dake daukar hankulansu duka, amma ba a tattauna sosai kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi kafa gwamnatin hadin kan al'umma da gyara tsarin mulkin kasa da sake gudanar da babban zabe da kuma yaki da ta'addanci ba.

Mistura ya bayyana fatan cewa, za a iya tattauna batutuwan nan hudu a shawarwari na gaba, wanda mai yiwuwa za a gudanar da shi a watan Yunin bana. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China