in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a fara shawarwari kan batun Syria karo na shida
2017-05-09 10:45:45 cri
Ofishin manzon musamman na babban sakataren MDD kan batun Syria, ya ce za a fara sabon tattaunawar wanzar da zaman lafiya a Syria, karkashin jagorancin MDD a ranar 16 ga wata a birnin Geneva na Switzerland.

Sanarwar da ofishin ya fitar a jiya Litinin ta ce, yayin tattaunawar da za a fara nan ba da jimawa ba, da ma sauran shawarwarin da za a gudanar a nan gaba, manzon na musamman Staffan de Mistura tare da sauran masu ruwa da tsaki, za su ci gaba da tattaunawa bisa kuduri mai lamba 2254 na kwamitin sulhu na MDD, inda a halin yanzu kuma, ake share fagen taron yadda ya kamata.

Staffan de Mistura ya kuma jaddada fatan cewa, za a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a birnin Astana a makon da ya gabata, a wani yunkuri na rage nuna karfin tuwo, ta yadda za a samar da yanayi mai kyau ga shawarwarin da za a fara.

Daga farkon shekarar bara har zuwa yanzu, an tattauna har sau biyar, karkashin jagorancin Staffan de Mistura, sai dai ana fuskantar sabanin ra'ayi sosai, abun da ya sa aka tsara wasu muhimman batutuwa da za a tattauna kansu.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China