Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR, ta yi gargadin cewa, muddin ba ta samu karin kudade ba, to za ta zaftare adadin iyalai dubu 60, daga cikin wadanda take baiwa tallafi na wata wata na 'yan gudun hijirar Syria dake kasashen Lebanon da Jordan a farkon wata mai kamawa.
Mai magana da yawun hukumar ta UNHCR, ya shedawa manema labarai cewa, wani muhimmin kaso na kudaden da ake bada taimakon ga 'yan gudun hijirar Syria ya samu gibi, kuma ana bukatar karin kudaden ne cikin gaggawa domin kaucewa rage adadin wadanda ke amfana da tallafin ceto rayuwar 'yan gudun hijirar na Syria a watanni hudun na biyu na wannan shekara.(Ahmad Fagam)