Za a gudanar da gasar wasannin motsa jiki na kasashen BRICS wato kasashen Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afirka ta Kudu daga ranar 17 zuwa 21 ga watan nan a birnin Guangzhou da ke lardin Guangdong na kasar Sin, gasar da ake fatan za ta kara inganta hadin gwiwa ta fuskar wasannin motsa jiki da mu'amala ta fuskar al'adu a tsakanin kasashen BRICS.
A yayin gasar da za a fara a karshen wannan makon da muke ciki, 'yan wasa za su fafata da juna a manyan wasanni guda 3 wato wasan kwallon kwando, kwallon hannu da wasan Kungfu. (Tasallah Yuan)