Jami'in ya bayyana hakan ne a jiya Juma'a, a lokacin taron koli na ministocin kudi da manyan bankuna na kasashen mambobin kungiyar BRICS, wanda ya gudana a Baden-Baden dake shiyyar kudu maso yammacin kasar Jamus.
Ministan kudin kasar Sin Xiao Jie, ya lura cewa kungiyar ta BRICS, wadda ta kunshi kasashen Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Africa ta Kudu, suna aiki kafada da kafada a ko da yaushe wajen zurfafa hadin gwiwarsu a fannin cigaban harkokin kudade, kuma suna samar da babbar gudunmowa wajen habaka cigaban BRICS da ma bunkasa hanyoyin gudanar da tattalin arzikin duniya baki daya.
Xiao ya ce, a wannan shekarar ta 2017, kasar Sin za ta cigaba da jajurcewa domin ganin hadin gwiwar BRICS ta kara habaka, kana za ta cigaba da zakulo hanyoyin karfafa hadin kai a fannonin hadin gwiwar gwamnatoci da hukumomi masu zama kansu, da habaka matakan gudanar da al'amurran kudi bisa yarjejeniya, da gudanar da bincike game da yadda harkokin kudaden ke gudana, da batun haraji, a matsayin wasu matakai da za su kara daga likafar hadin gwiwar tafiyar da al'amurran kudi ya zuwa sabon mataki.(Ahmad Fagam)