Wakilan sun gabatar da wannan kuduri ne a jiya Alhamis, yayin taro karo na biyu na kwanaki biyu da suka gudanar a birnin Qingdao na lardin Shandong dake gabashin kasar Sin.
Mahalarta taron sun yi bitar nasarorin da aka samu a fannin hadin gwiwar kasashe mambobin kungiyar ta BRICS, musamman a fannonin siyasa, da tsaro, da tattalin arziki, tare da musaya ta al'adu da jama'a tsakanin sassan kasashe mambobin ta.
Sun kuma nazarci shirye shirye da ake gudanarwa, game da taron kungiyar na bana, wanda ke tafe tsakanin ranekun 3 zuwa 5 ga watan Satumba a birnin Xiamen dake lardin Fujian.
Mahalarta taron sun kuma jinjinawa kasar Sin, game da jagoranci managarci da take baiwa BRICS, yayin da take rike da kujerar karba karba ta shugabancin kungiyar a bana, sun kuma tabbatar da aniyar su, ta marawa kasar baya, a yunkurin cimma nasarar taron birnin na Xiamen wanda ke tafe nan da 'yan watanni. (Saminu)