in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kira taron dandalin tattaunawa tsakanin jam'iyyu da kwararru da kungiyoyin al'umma na kasashen BRICS
2017-06-11 13:50:40 cri
A jiya Asabar, aka gudanar da taron dandalin tattaunawa tsakanin jam'iyyu da kwararru da kungiyoyin al'umma na kasashen BRICS a birnin Fuzhou dake kudancin kasar Sin, taron wanda ya kasance irinsa na farko da ya gudana, a tsakanin jam'iyyun siyasa da kwararru da ma kungiyoyin al'umma tun bayan kafuwar tsarin hadin gwiwar kasashen BRICS. Mahalarta taron suna ganin cewa, a cikin shekaru 10 da suka wuce, kasashen BRICS sun gudanar da hadin gwiwa a fannoni da dama, tare kuma da cimma kyawawan nasarori. A yayin da ake fuskantar rashin tabbas ta fannonin siyasa da tattalin arziki a duniya, ya kamata tsarin hadin gwiwar kasashen BRICS ya taka rawar jagoranci, don samar da gudummawarsa wajen gudanar da harkokin duniya.

Sashen kula da hulda da kasashen waje na kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ne ya kira wannan taron dandali, kan yunkurin inganta tuntubar juna da hada karfi da karfe, don inganta hadin gwiwar kasashen BRICS da kuma ba da shawarwari ga taron kolin kasashen BRICS da za a gudanar a birnin Xiamen da ke kudancin kasar Sin.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China