in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fidda tsarin aiki yayin kammalar taron masu ruwa da tsaki a fannin yada labarai na kungiyar BRICS
2017-06-08 20:08:49 cri

Dandalin watsa labarai na kungiyar BRICS ya kammala a Alhamis din, bayan da mashiryansa 27, suka amince da wani tsarin gudanar da ayyukan hadin gwiwa a fannin yada labarai.

Dandalin wanda aka yiwa lakabi da "Fadada hadin gwiwa a fannin yada bayanai na BRICS, tare da tabbatar da adalci a bangaren batutuwa da suka shafi kasa da kasa," kamfanin dallancin labarai na kasar Sin Xinhua ne ya gabatar da shawarar aiwatar da shi, da hadin gwiwar rukunin CMA na Brazil, da kamfanin dillancin labarai na Rasha Sputnik. Sauran sun hada da rukunin watsa labarai na Hindu Group dake kasar Indiya, da kuma wata kafar watsa labarai mai zaman kanta dake Afirka ta kudu.

Tsarin ayyukan da dandalin ya fitar dai ya ce ya kamata a fadada hadin gwiwar kasashen BRICS a fannin yada labarai bisa bukatun kasashe mambobin kungiyar.

Da yake tsokaci game da hakan, babban editan kamfanin dillancin labarai na Xinhua He Ping, ya ce kudurorin da aka sanya gaba cikin tsarin ayyukan, sun hada da yunkurin sauke nauyin dake wuyan su na aikin wayar da kan al'umma, tare da samarwa al'umma zarafin furta albarkacin bakin su.

Ana kuma sa ran tsarin zai bada damar gaggauta bunkasa harkokin yada labarai tsakanin kasashe mambobin kasashen BRICS.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China