A yayin taron wanda aka fara a jiya, mahalarta sun mayar da hankali matuka gami da gudanar da shawarwari kan yanayin siyasa da tattalin arziki na duniya, da kuma cimma maslaha kan manyan ayyuka hudu da za su gudanar a bana, wadanda suka hada da, inganta hadin-gwiwa ta fuskokin siyasa, tattalin arziki da kuma mu'amala tsakanin al'umma.
A ranar 1 ga watan Janairun bana ne, kasar Sin ta karbi shugabancin karba-karba na kungiyar BRICS, haka kuma daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Satumbar bana, za'a gudanar da taron shugabannin kasashen BRICS karo na 9 a birnin Xiamen na lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar Sin,
A nasu bangaren kuma, wakilai mahalarta taron a wannan karo a birnin Nanjing, sun yabawa rawar da kasar Sin ta taka a matsayinta na shugabar karba-karba ta kungiyar, kana sun yarda da babban jigon taron da aka tsara, gami da batutuwan da za'a tattauna a wajen taron shugabannin kungiyar da za'a yi a watan Satumba a birnin na Xiamen da ke nan kasar Sin.(Murtala Zhang)