Kwanan baya, bankin duniya ya kaddamar da hasashensa kan tattalin arzrikin duniya a shekarar 2017, inda ya nuna cewa, saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Habasha zai kai kashi 8.3 cikin dari a bana, wanda ba a ga irinsa a nahiyar Afirka ba. Kasashen Tanzaniya, Kwadibuwa da Senegal za su sama na biyu, na uku da na hudu saboda samun saurin ci gaban tattalin arziki na kashi 7.2 cikin dari, kashi 6.8 cikin dari, da kashi 6.7 cikin dari. Jarin da gwamnati take zubawa, shi ne muhimmin dalilin da ya sa saurin bunkasuwar tattalin arzikin wadannan kasashe.
A sa'i daya kuma, kasar Amurka ta rage tallafin da take bai wa kasashen Afirka, wanda ya sa tabarbarewar tattalin arziki a wasu kasashen Afirka da ma wasu kasashe marasa ci gaban tattalin arziki. Sa'an nan tsananin fari da ake fama da shi a yankin gabashin Afirka ya kawo wa yankin babban kalubale a fannonin aikin gona da samun isasshen abinci. (Tasallah Yuan)