in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya gana da takwaransa na kasar Habasha
2017-05-13 13:35:04 cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya gana da takwaransa na kasar Habasha Hailemariam Dessalegn a babban dakin taron jama'a dake birnin Beijing.

Mr. Dessalegn ya zo kasar Sin ne domin halartar taron koli na dandalin hadin gwiwar kasa da kasa game da shawarar "Ziri daya da hanya daya" da za a bude a birnin Beijing.

A yayin ganawar ta su da yammacin jiya Jumma'a, Li Keqiang ya ce kasar Sin na goyon bayan kasar Habasha, wajen raya harkokin masana'antu da ayyukan noma na zamani, inda ta ke son taimaka mata a fannin sha'anin kudi da kuma horas da ma'aikata, ta yadda kasar Habasha za ta samu dauwamammen ci gaba.

Haka zalika, Firaminista Li ya ce, ya kamata kasar Habasha ta dukufa wajen aiwatar da shirin habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta fuskar ayyukan masana'antu da samar da ababen more rayuwa da sauran wasu bangarori ta yadda za a mori juna.

A nasa bangare kuma, Mr. Dessalegn ya nuna cewa, kasashen Afirka suna da buri iri daya da kasar Sin a fannin neman ci gaba, kuma a halin yanzu, ana samun kyawawan sakamako bisa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasar Habasha a fannin raya ayyukan masana'antu da samar da ababen more rayuwa, lamarin da ya ba da gudummawa matuka ga kasar Habasha wajen inganta ayyukan masana'antu da harkokin noma na zamani.

Firaministan na Habasha ya kara da cewa, a nan gaba, kasar za ta kafa sabon cibiyar jiragen sama, inda za ta saye jiragen da kasar Sin ta kera. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China