in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta tallafawa shirin WFP a Habasha
2017-04-28 10:53:18 cri
Gwamnatin kasar Sin ta mika tallafin kayan abinci mai kunshe da sinadaran gina jiki, na kimanin dalar Amurka miliyan 8, karkashin shirin samar da abinci na MDD ko WFP, a wani mataki na agazawa al'ummun da fari ke addaba a Habasha.

Ana sa ran wannan tallafi zai bada damar kai dauki, ga sama da yara kanana da mata da yawan su ya kai 277,000 dake fama da tamowa a kasar dake gabashin Afirka.

Da yake jawabi yayin mika kayan, jakadan kasar Sin a Habasha La Yifan, ya ce, Sin kawa ce ga kasashen Afirka, a kuma ko da yaushe tana fatan taimaka wa nahiyar iyakacin karfin ta.

Daga nan sai ya ja hankalin sauran kasashen duniya, da su cika alkawuran su, game da dakile sauyin yanayi, wanda shi ne mataki mafi dorewa na kare aukuwar bala'u kamar fari, dake addabar wasu yankuna na kahon Afirka.

A nasa tsokaci kuwa, babban jami'in shirin na WFP a Habasha John Aylieff, jinjinawa kasar ta Sin yayi, bisa tallafin ta, yana mai cewa tallafi ne da ya zo lokacin da Habasha ke shan fama da fari, wanda bata taba fuskantar makamancin sa cikin shekaru 50 da suka gabata ba.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China