Kwarraren ya ce , bankin zai taimakawa kasar ta Habasha samun kudaden da za ta aiwatar da ayyukan samar da kayayyakin more rayuwar jama'a da samar da kasuwannin da za ta rika fitar da kayayyakin da ta sarrafa.
A nasa jawabin firaministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn ya yaba da shigar kasar tasa cikin bankin na AIIB, yana mai cewa, amincewar da bankin da ya yiwa kasarsa, ya saukakawa kasar samun isassun kudaden gudanar da ayyukanta daban-daban.
Kasar Sin ce dai ta kirkiro kafa bankin da nufin magance bukatun muhimman kayayyakin more rayuwa, kuma kasar Habasha tana iya samun rance da sauran taimako game da ayyukanta na kayayyakin more rayuwa.
A shekarar 2015 ne kasar Habasha ta mika takardar neman zama mamban bankin, kana daga bisani bankin ya tantance wannan bukata, inda a ranar Asabar din makon da ya gabata aka amince da kasar Habashan a matsayin kasa ta uku daga nahiyar Afirka da ta zama mamba a wannan Bankin, bayan kasashen Afirka ta kudu da kuma Masar. (Ibrahim)