in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin jiragen saman Habasha ya kara yawan jiragensa dake zuwa kasar Sin kai tsaye
2017-05-22 09:44:53 cri
Kamfanin jiragen saman Habasha wato Ethiopian Airlines, ya kara adadin jiragensa dake zuwa kasar Sin kai tsaye duk mako, zuwa 34.

An samu karuwar adadin ne biyo bayan fara tashin jiragen zuwa Chengdu babban birnin lardin Sichuan, sau uku a sati.

Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da tashin jirgin farko zuwa Chengdu, a harabar filin jirgin saman kasa da kasa na Habasha, babban jami'in ofishin Jakadancin kasar Sin a Habasha Liu Tao, ya ce kasancewar Chengdu cibiyar al'adu da tattalin arziki, zuwan jiragen zai inganta harkokin noma da cinikayya da bude ido da kuma hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da sauran sassan duniya, inda Habasha za ta kasance gada dake sada kasashen.

A nasa jawabin, shugaban sashen kasuwanci na kamfanin Busera Awol, ya ce wannan sabon ci gaba ne ga daddadiyar huldar dake tsakanin kasashen biyu tun bayan fara tashin jiragen kasar Habasha zuwa Beijing a shekarar 1973.

Kamfanin jiragen saman Ethiopia shi ne kamfani na farko a Afrika, kuma na hudu a duniya da jirginsa ya fara zuwa kasar Sin a shekarar 1973.

Baya ga kaddammar da fara tashin jiragen zuwa Chengdu sau uku a sati, a yanzu haka jiragen kamfanin na tashi kai tsaye a kullum zuwa Beijing da Guangzhou da Shanghai da Hongkong. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China