in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi garkuwa da mutane 20 a harin da aka kai a Somaliya
2017-06-15 13:20:38 cri
A jiya Laraba ne, rundunar 'yan sandan kasar Somaliya ta sanar da cewa, ya zuwa yanzu harin boma-boman da aka kai a babban birnin kasar, Mogadishu ya haddasa rasuwar mutane a kalla guda 14, haka kuma, bayan aukuwar harin, maharan sun yi garkuwa da mutane a kalla guda 20, domin shawo kan 'yan sandan. Amma, a halin yanzu, ba a tabbatar da halin da suke ciki ba.

Haka kuma, 'yan sandan sun bayyana cewa, maharan sun kashe wutar lantarki a dakin cin abincin da suka kai harin, kuma, 'yan sanda ba su yi nasarar kama su ba, saboda duhun dare. Amma, a halin yanzu, 'yan sandan sun killace yankin gaba daya.

Kungiyar Al Shabaab ta kasar Somaliya ta sanar da daukar alhakin kai wannan hari. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China