in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 8 sun rasu sakamakon harin da aka kaddamar a Somaliya
2017-06-15 10:53:26 cri
A daren jiya Laraba, an kai hari a wani dakin cin abinci dake yankin Hodon a babban birnin kasar Somaliya, Mogadishu. Harin da ya haddasa rasuwar mutane a kalla 8.

Bisa labarin da aka samu, an ce, maharin ya shiga dakin cin abincin ne da mota, wadda aka dasa boma-bomai a cikinta, inda fashewar boma-boman ta haddasa rasuwar mutanen.

Haka kuma, an ce, galibin mutanen da suka je dakin cin abincin, jami'an gwamnatin kasar ne da kuma wasu matasa.

Ya zuwa yanzu, babu wata kungiyar da ta sanar da daukar alhakin kaddamar da wannan hari. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China