in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somalia ta yiwa dokar yaki da rashawa gyaran fuska
2017-05-22 09:43:19 cri
A jiya Lahadi gwamnatin Somaliya ta ba da wata sanarwa, inda ta ce yanzu ita da wasu kwararru na dubawa dokokin yaki da rashawa na kasar, kuma a nan gaba kadan ne za'a gabatarwa majalisar dokokinn kasar don ta nazarci dokokin kana ta amince da su.

Sanarwar da ma'aikatar yada labarai da raya al'adu da yawon shakatawa ta kasar ta fitar, ta bayyana cewa, gwamnatin kasar a shirye take ta yaki da rashawa a dukkannin matakai a kasar.

Ya zuwa wannan lokaci, sabuwar gwamnatin Somali tana yunkurin aiwatar da shirye shiryen yaki da rashawa a kasar.

Kawo yanzu, ma'aikatar ta lissafta wasu daga cikin irin nasarorin da wannan gwamnatin ta cimma da suka hada da kara yawan kudaden haraji tun daga ranar 18 ga watan Faburairu sakamakon tsauraran matakai da gwamnatin ta dauka game da sha'anin kudi, hakan ya samar wa gwamnatin kasar kudaden shiga masu yawan gaske wadanda za ta yi amfani da su a ayyukanta.

Gwamnatin Somali ta nanata aniyarta na cigaba da daukar matakan yin garambawul a fannin gudanar da al'amurran kudin kasar, saboda kamar yadda ta ambata, tana da masaniya game da yadda aka dinga yin sakaci wajen hukunta masu aikata laifukan rashawa a lokacin gwamnatocin baya.

Sai dai a halin yanzu, sabuwar gwamnatin ta ce za ta dauki dukkan matakan da suka dace wajen tafiyar da dukiyar kasa bisa doka da oda. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China