in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somaliya da AU sun sake karbe ikon yankunan kudancin kasar
2017-05-28 12:16:04 cri
Rundunar sojin kasar Somaliya SNA, wanda ke samun goyon bayan dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika AU, a jiya Asabar sun sake kwace ikon wasu yankuna da dama a kudancin kasar Somaliyan.

Ministan yada labarai na jihar kudu maso yammacin kasar Ugaas Hassan, shi ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar hannu, inda ya ce dakarun tsaron na hadin gwiwa sun yi nasara a samamen da suka kai arewaci da kudancin garin Baidoa.

SNA, da AMISCOM da dakarun wanzar da tsaro na kudu maso yammacin jihar, sun yi nasarar kwato yankuna masu yawa a arewaci da kudancin garin Baidoa, ciki har da yankin Gof-gudud, wanda yake karkashin ikon mayakan 'yan ta'adda a 'yan kwanakin da suka gabata, Hassan ya tabbatar da hakan.

Ya kara da cewa, babu sauran wajen buya ga mayakan 'yan ta'addan kuma aikin farautar tasu zai ci gaba.

AMISOM na nufin dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika dake Somaliya, wanda kungiyar tarayyar Afrikar ta kafa bisa amincewar MDD domin gudanar da ayyukan tabbatar da tsaron shiyyoyi.

Mayakan Al-Shabaab sun kwace ikon yankin Gof-gudud mai tazarar kilomita 35 daga arewacin yankin Bay ne, a ranar 9 ga watan Mayu. Kuma sun hallaka a kalla sojojin Somaliya 6 kana sun jikkata wasu da dama a sanadiyyar wani bam da suka dasa a yankin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China