in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun musamman na kasar Somaliya sun tarwatsa sansanin bada horo na Al-Shabaab
2017-06-12 10:23:57 cri
Shugaban kasar Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed, wanda aka fi sani da Farmajo, ya bayyana cewa ya umarci wata tawagar dakarun tsaro na musamman wadanda suka tarwatsa babban sansanin horas da sojoji na mayakan kungiyar Al-Shabaab dake tsakiyar Jubba a kudancin Somaliya.

Farmajo ya bayyana cewa a ranar Lahadi ne dakarun suka wargaza sansani dake kusa da Sakow bayan harin da suka kaddamar ya samu nasara, kana sun yi nasarar lalata babbar tungar mayakan na Al-Shabaab.

Cikin wata sanarwar da shugaban Somaliya ya fitar a Mogadishu ya ce, ya umarci wannan runduna ta musamman ne tare da tallafin dakarun tsaron hadin gwiwa na kasa da kasa don yin luguden wuta kan babban sansanin horas da sojoji na Al-Shabaab dake kusa da Sakow, a tsakiyar yankin Jubba. Ya kara da cewa, wannan hari zai yi matukar dakile shirin abokan gaba wajen hana su samun damar kaddamar da sabbin hare hare a cikin kasar Somaliya.

Da ma dai shugaban na Somaliya ya fada a lokacin rantsuwar kama aiki cewa, babban abin da gwamnatinsa za ta fi baiwa fifiko, batun matsalar tsaro, kana ya bayyana cewa kaddamar da harin na ranar Lahadi wani mataki ne da zai rage barazanar hare-haren mayakan Al-Shabaab. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China