Bugu da kari, ya ce, Theresa May ta aika wasiku ga sauran mambobin kungiyar EU 27, inda ta sanar da su cewa, kasar Burtaniya ta tsai da kudurin fara aiwatar da shirin ficewar kasar daga kungiyar EU, kuma Burtaniya tana sa ran yin shawarwari da EU kan batun cikin sauri.
A ranar 13 ga watan nan da muke ciki, majalisar dokoki Burtaniya ta zartas da daftarin ficewar kasa daga kungiyar EU, lamarin da ya sa, aka kawar da dukkan matsalolin dake gaban kasar ta fuskar dokoki wajen fara aiwatar da shirin ficewarta daga kungiyar EU.
Bugu da kari, sarauniyar Ingila Elizabeth II ta riga ta sa hannu kan daftarin, inda ta amince da firaministar kasar Theresa May da ta fara wannan aiki. (Maryam)