in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin kasar Sin ya yi kira da a kara lura da kasar Somaliya
2017-05-18 13:04:48 cri

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin da ke MDD Wu Haitao ya bayyana a yayin taron kwamitin sulhun kan batun Somaliya da aka kira jiya Laraba 17 ga wata, cewar ya zuwa yanzu, kasar Somaliya na fama da kalubaloli masu tsanani a fannonin siyasa, tsaro, tattalin arziki, da ma jin kai. Akwai 'yan kasar kimanin miliyan 6.2 da ke fama da karancin abinci, kuma kusan mutane miliyan uku ne ke bukatar taimakon gaggawa a wannan fanni.

Mr. Wu ya kara da cewa, kasar Somaliya za ta kwashe dogon lokaci kafin ta cimma burin samun kwanciyar hankali mai dorewa, da na bunkasuwar tattalin arzikinta. Don haka ya kamata kasashe daban daban su ci gaba da lura da kasar da kuma mara mata baya.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China