in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gabatar da tambarin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta yanayin sanyi ta Beijing kafin karshen shekarar bana
2017-06-14 10:50:09 cri
A jiya Talata ne, aka gudanar da taron manema labarai, bayan taron kwamitin kula da harkokin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta lokacin sanyi wadda za a yi a shekarar 2022 a nan birnin Beijing, inda mataimakin shugaban birnin Beijing, kana mataimakin shugaban kwamitin gudanarwar harkokin gasar wasanin motsa jiki ta Olympics ta yanayin sanyi ta Beijing Zhang Jiandong ya bayyana cewa, za a gabatar da tambarin gasar wasannin motsa jikin ta Olympics, da kuma tambarin gasar wasannin Olympics ta nakasassau ta lokacin sanyi kafin karshen shekarar bana.

Zhang Dongjian ya ce, kwamitin gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta yanayin sanyi ta Beijing, zai gudanar da ayyukansa bisa ka'idodjin kiyaye muhalli, da hadin gwiwa, da bude kofa ga waje, ba kuma tare da barnata kudade ba, domin ciyar da ayyukan gaba yadda ya kamata. Haka kuma, ya ce, a nan gaba, za a gaggauta ayyukan ginawa, da gyara dakunan wasannin motsa jiki, da samar da ilmi game da wasannin motsa jiki a yanayin sanyi, da kuma ciyar da ayyukan gudanar da gasar wasannin Olympics ta nakasassau gaba, domin tabbatar da gudanar da gasannin biyu yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China