in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shiga mataki na karshe na neman iznin daukar bakuncin gasar wasannin Olympics ta 2024
2017-02-05 13:31:36 cri

A ranar 3 ga wata, biranen Los Angeles da Paris da Budapest sun mika takardun karshe na neman iznin karbar bakuncin gasar wasannin Olympics ta shekarar 2024 ga kwamitin shirya gasar wasannin Olympics ta duniya wato IOC, lamarin da ya sheda cewa, an shiga mataki na karshe na neman iznin karbar bakuncin gasar tsakanin biranen uku.

Takardun da biranen uku suka mika a wannan karo sun hada da fannonin gudanar da wasanni, da yadda ake ji a zuciya game da gasar, da kuma sake yin amfani da filayen wasa bayan kammala gasar.

An ce, za a yi bincike ga biranen uku bi da bi ne daga watan Afrilu zuwa Mayu na bana, kuma kwamitin IOC zai jefa kuri'u don tsaida kudurin bada iznin ga kowane birni a yayin cikakken zama da za a gudanar a birnin Lima na kasar Peru a watan Satumba na bana.

A cikin shirin neman iznin daukar bakuncin gasar na birnin Paris, kashi 95 cikin dari na filayen wasa ko dakunan wasan tsofaffi ne ko kuma na wucin gadi ne, mashahurran gine-gine da wurare dake cibiyar birnin Paris za su zama wurin wasanni. Birin Los Angels zai yi amfani da yawancin filayen wasa da aka riga aka gina su a da. Bisa sabon binciken da aka yi a tsakanin jama'ar kasar Hungary, kashi 63 cikin 100 na jama'a sun nuna goyon baya ga birnin Budapest da a ba shi iznin daukar bakuncin gasar wasannin Olympics. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China