Ranar 8 ga wata ne babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya sanar da nada mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Liu Zhenmin, a matsayin sabon mataimakin sa mai kula da harkokin tattalin arziki da zamantakewar al'umma, inda zai maye gurbin Wu Hongbo, mai rike da mukamin a yanzu. Wa'adin aikin mista Wu Hongbo zai cika ne a ranar 31 ga watan Yulin bana.
Yanzu Liu Zhenmin, shi ne mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin mai kula da harkokin nahiyar Asiya, da dokoki, da yarjeniyoyi, da iyakokin kasa da na teku. (Tasallah Yuan)