in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Sin sun bayar da gudummawa sosai wajen gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD
2016-07-21 10:18:27 cri
A ranar 10 ga wata ne aka kaiwa sojojin kasar Sin da ke aikin kiyaye zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu harin bam, yayin da suke aiki a sansanin 'yan gudun hijira na MDD dake kasar, wanda ya haddasa mutuwar sojojin Sin biyu Li Lei da Yang Shupeng, yayin da sojojin Sin guda biyar suka ji rauni.

A cikin shekaru 26 da sojojin Sin suka kwashe suna aikin kiyaye zaman lafiya, yawan sojojin kasar da suka mutu a yayin da suke gudanar da wannan aiki ya kai 13.

Ya zuwa yanzu, sojojin Sin 2496 ne suka gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a cibiyar MDD da yankuna 9, ciki har da rukunonin kiyaye zaman lafiya 14 da suka kunshi sojojin injiniya da jigilar kayayyaki da ba da jinya da ba da kariya da sojojin kasa da yawansu ya kai 2403, da kuma hafsoshi da masu binciken aikin soja 93.

Wadannan yankuna 9 sun hada da Congo Kinshasa, Liberia, Sudan ta Kudu, yankin Darfur dake kasar Sudan, Lebanon, Mali, yankin Gabas ta Tsakiya, yammacin Sahara, da kuma Cote d'Ivoire.

Kasar Sin kasa ce da ta fi sauran kasashe 5 dake da kujerun din-din-din a kwamitin sulhun MDD tura sojojin kiyaye zaman lafiya, kana yawan kudin da ta samar ga MDD a shekarar 2016 domin gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya ya kai dala miliyan 844, wanda ya kai kashi 10.2 cikin dari bisa na adadin kudaden da ake kashewa a wannan fanni, wanda ya kai matsayi na biyu a cikin kasashe membobin MDD.

Haka kuma a yabawa sojojin kiyaye zaman lafiya na Sin yayin da suke gudanar da ayyukansu a sassa daban-daban na duniya. Kuma yadda sojojin Sin suke gudanar da ayyukansu cikin hanzari, inganci da bin ka'idojin da Sin ta gindaya sun zama abin misali a yankunan da suke gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China