in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nuna goyon baya ga hadin gwiwar kungiyar kasashen musulmi da MDD
2016-11-18 16:25:36 cri
Zaunannen wakilin Sin dake MDD Liu Jieyi ya bayyana a jiya Alhamis 17 ga wata cewa, Sin na goyon bayan ci gaba da raya hadin gwiwa tsakanin kungiyar kasashen musulmi da kuma MDD, tare da raya tsarin kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa, don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya gaba daya.

Kwamitin sulhun MDD ya gudanar da taron sanar da inganta dangantakar kawance tsakanin MDD da kungiyar kasashen musulmi, a fannin yaki da tsattsauran ra'ayi. Game da hakan Mr. Liu Jieyi ya bayyana cewa, Sin da kasashen musulmi na sada zumunta mai karko, da yin hadin gwiwa da juna sosai. Kaza lika Sin na dora muhimmanci sosai ga muhimmiyar rawar da kungiyar kasashen musulmi ke takawa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China