in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bukaci kasashen duniya su hada hannu wajen kare al'adun yankunan dake fama da rikici
2017-03-25 12:47:23 cri

Wakilin kasar Sin na dindindin a MDD Liu Jieyi, ya bukaci kasashen duniya, su kara kaimi tare da hada hannu, domin kare al'adu a yankunan da ke fama da rikici.

Da yake jawabi a jiya Jumma'a, yayin taron kwamitin sulhu na MDD kan kare al'adu daga ayyuakan 'yan ta'adda, Liu Jieyi ya jadadda bukatar al'ummomin duniya su hada hannu wajen tabbatar da karewa da alkinta al'adu a yankunan dake fuskantar rikici.

Wakilin ya ce ya kamata a yi kokari wajen mara baya ga yankunan da ke fama da rikici ta yadda za su bunkasa matakan kare kawunansu, yana mai kira da kasashen dake fama da rikice-rikice su samar da dabarun kare kai da yin gargadin cikin lokaci, tare da inganta matakan kare al'adu.

Liu Jieyi, ya ce ta'addanci ya zama babbar barazanar da alkinta al'adu ke fuskanta a yankunan da ake fama da tashe-tashen hankula.

A don haka, ya bukaci al'ummomin duniya su aiwatar da kudurin kwamitin mai lamba 2347 mai nufi kare al'adu da fadada ayyukan kwamitin masu alaka da lamarin da samar da wani tsarin samun bayanai tare kuma da murkushe ayyukan 'yan ta'adda ta yadda za a dakile barazanar da suke wa al'adu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China