Cikin jawabinta, Liu Hua ta jaddada cewa, zaman lafiya shi ne babban tushen inganta da kuma kare hakkin dan Adam, sa'an nan ta gabatar da manufofi guda biyar kan yadda za a shimfida zaman lafiya na dindindin da kuma inganta ayyukan kare hakkin dan Adam, wadannan manufofin biyar sun hada da, gina dangantakar abokantaka cikin yanayin adalci, warware sabanin dake tsakanin sassa daban daban ta hanyar zaman lafiya, kiyaye zaman lafiya ta hanyar yin hadin gwiwa, neman ci gaba domin inganta yanayin zaman lafiyar duniya, da kuma girmama al'adu iri daban daban.
A jiya ne aka fara taron kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD karo na 34 a birnin Geneva, wanda za a kammala a ran 24 ga wata Maris mai zuwa. Kuma babban taken taron na wannan shekara shi ne "karfafa shawarwari da hadin gwiwar kasa da kasa, ta yadda aikin kare hakkin dan Adam zai tabbatar da zaman lafiyar duniya". (Maryam)