Mista Hervé Ladsous ya bayyana cewa, kasar Sin ita ce kasar da ke kujerar din-din-din a kwamitin sulhun MDD da ta fi tura sojojin da ke aikin kiyaye zaman lafiya na MDD. Ya zuwa yanzu, ta zama ta biyu a fannin zuba jari kan aikin kiyaye zaman lafiya. Ya ce, sojojin kiyaye zaman lafiya na Sin suna da kayayyakin zamani, da horaswa mai inganci, wannan ya sa suke gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya yadda ya kamata. Ban da gudanar da ayyukansu kamar yadda MDD ta tsara, suna kuma sada zumunci da fararen hula a yankunan da suke gudanar da ayyukansu.
Alkaluman da MDD ta bayar, sun nuna cewa, kawo yanzu Sin ta tura sojojin kiyaye zaman lafiya sama da dubu uku zuwa kasashen Sudan ta Kudu, Lebanon, Mali da sauransu domin gudanar da wannan aiki. Daga shekarar 2016 zuwa 2018, Sin za a biya kashi 10.2 cikin dari na jimillar kudaden da za a kashe wajen gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD, wadda take bin bayan kasar Amurka.(fatima)