Tun daga shekarar 1948 zuwa yanzu, aikin tabbatar da zaman lafiya na MDD ya zama wata muhimmiyar hanyar da kasashen duniya ka amfani da ita wajen daidaita matsalolin dake yin barazana ga zaman lafiya da tsaron duniya. Ya zuwa yanzu, kasashe membobin MDD 123 sun tura sojoji da 'yan sanda domin halartar ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD.
Rahotanni na cewa, tun daga shekarar 1990 lokacin da Sin ta halarci aikin kiyaye zaman lafiya na MDD karo na farko zuwa yanzu, baki daya kasar ta tura sojoji sama da dubu 30 domin shiga wannan aikin, wadda ta zama kasar da ke kujerar din-din-din a kwamitin sulhun MDD da ta fi tura sojojin a wannan aiki. Wannan ya nuna cewa, Sin ta cika alkawarinta na tabbatar da zaman lafiya a duniya, tare da kare mutuncinta na daukar nauyi a kasashen duniya.(Fatima)