in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya kammala ziyarar aiki a Turai
2017-06-04 13:13:46 cri
A ranar Asabar, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya dawo birnin Beijing, bayan da ya kammala rangadin aikinsa a kasashen Jamus da Belgium, inda ya gudanar da shawarwarin shekara-shekara da shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel, da kuma halartar ganawa karo na 19 tsakanin shugabannin kasar Sin da kungiyar tarayyar Turai.

Manyan jami'an kuniyar tarayyar Turai da gwamnatin Belgium, da jakadiyar kasar Sin dake kungiyar tarayyar Turai Yang Yanyi, gami da jakadan kasar Sin dake kasar Belgium Qu Xing sun yi ban kwana da firaminista Li a filin saukar jiragen sama a birnin Brussels na kasar Belgium.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China