Dakarun gwamnatin Nijer sun hallaka masu dauke da makamai 'yan kungiyar Boko Haram su 50
Bisa labarin da kafofin watsa labarun Nijer suka bayar a jiya Litinin, an ce, a daren ranar 9 zuwa asubahin ranar 10 ga wannan wata, dakarun gwamnatin kasar sun yi musayar wuta da masu dauke da makamai 'yan kungiyar Boko Haram wadanda suka kai hari a lardin Diffa dake kudu masu gabashin kasar, inda aka hallaka masu dauke da makamai a kalla 50 na mayakan Boko Haram din. Sannan wasu sojojin gwamnati fiye da 10 suka jikkata.
Daga baya dakarun gwamnatin kasar Nijer sun cigaba da farautar masu dauke da makamai na Boko Haram wadanda suka ranta ana kare, kana dakarun suna gudanar da bincike a yankunan ta sararin sama.
Tun daga karshen watan Yulin shekarar 2016 ne, rundunar sojin kasashen Najeriya, da Nijer da Chadi da Kamaru suka fara farautar 'yan kungiyar Boko Haram a yankunan dake kan iyakar Najeriya da Nijer. (Sanusi Chen)