Da yake tabbatar da hakan ga 'yan jarida a jiya, kwamandan rundunar sojin kasa mai kula da ayyukan soji a yankin Lucky Irabor, ya ce wasu mayakan kama su aka yi, yayin da wasu kuma suka mika kan su ga jami'an tsaro. Irabor ya ce tuni wasu daga cikin su suka amince da kasancewa mayakan kungiyar ta Boko Haram, kuma ana shirin gurfanar da su gaban kuliya domin fuskantar shari'a.
A daya bangaren kuma, Irabor ya ce gwamnatin Najeriya na shirin aiwatar da manufar sauya tunanin wani rukuni na mutanen da ake tsare da su, domin ba su damar sake komawa cikin al'umma ba tare da wata matsala ba.
Rikicin Boko Haram dai ya sabbaba kisan mutane da yawan su ya haura 20,000, tare da raba wasu miliyan 2.3 da muhallan su, tun daga shekarar 2009 ya zuwa wannan lokaci.
Sai dai a baya bayan nan gwamnatin Najeriya ta cimma manyan nasarori a yakin da take yi da kungiyar, inda a watan Janairu dakarun sojin kasar suka kori mayakan daga dajin Sambisa, dake matsayin babbar tungar kungiyar.(Saminu Alhassan)