Yayin taron manema labarai na kulla-yaumin, kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ce sabon rahoton ya bayyana irin tasirin da tabarbarewar tsaro da ayyukan jin kai ya yi a kan yara a kasar, tsakanin watan Junairun 2013 zuwa Decemban 2016.
Wakiliyar Sakatare Janar din na musammam kan harkokin yara da rikice-rikice Virginia Gamba, ta ce ayyukan Boko Haram sun jefa matsanancin tsoro a zukatan yaran dake yankin arewa maso gabashin Nijeriya da kasashe makwabta.
Tsakanin lokacin hada rahoton, hare-haren Boko Haram kan al'ummomi da arangama tsakaninta da Jami'an tsaro, sun yi sanadin mutuwar yara 3,900 tare da jikkata wasu 7,300.
Nijeriya dai, ta samu gagarumin nasara a yaki da take da Boko Haram, inda jami'an tsrao dake yankin da al'amarin ya fi kamari su ka fatattaki mayakan daga maboyarsu dake dajin Sambisa. (Fa'iza Mustapha)