Aisha Alhassan, ta bayyana hakan ne a yayin taron manema labaru a Abuja, babban birnin kasar, tace daga bisani za'a kai 'yan matan wajen bincike game da yanayin tunaninsu.
Ministar tace, tuni aka watsa hotunan 'yan matan 82 domin iyaye su tantance 'ya'yansu kasancewa akwai sunayen dake kamanceceniya da juna.
Aisha ta musanta rahotannin dake cewa ba za'a bar iyayen yaran ganin 'ya'yansu ba, sai dai tace ba kullum ne za'a dinga barin iyayen samun damar ganin 'ya'yan nasu ba.
Haka zalika minister tace gwamnatin Najeriya ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen neman maslaha game da yadda za'a sako ragowar 'yan matan na Chibok da ake tsare dasu.
Ta kara da cewa dukkan 'yan matan zasu koma makaranta a watan Satumba ciki har da yara matan 82 na baya bayan nan da aka sako, sannan za'a koya musu sana'o'i.